BAMBANCI DA KAMANCE TSAKANIN MIYAR GARGAJIYA DA TA ZAMANI

QUMSHIYA

BABI NA XAYA
1.0       Gabatarwa
1.1       Bitar ayukkan da suka gabata
1.2       Hujjar ci gaba da bincike
1.3       Hanyoyin gudanar da bincike
1.4       Muhallin bincike
1.5       Muhimmancin bincike
1.6       Naxewa

BABI NA BIYU
2.0 Shimfixa
2.1- Ma’anar miya
2.2- Abubuwan da ake tanada wajen haxa miyar gargajiya
2.3- Abubuwan da ake tanada wajen haxa miyar zamani
2.4- Sanadaran haxa miyar gargijiya
2.5- Sanadaran haxa miyar zamani
2.6- Naxewa

BABI NA UKKU
3.0-  Shimfixa
3.1- Yadda ake dafa miyar gargajiya
3.2– Yadda ake dafa miyar zamani
3.3– Bambancin miyar gargajiya da ta zamani
3.4– Kamance da ake samu tsakanin miyar gargajiya da ta zamani
3.5– Naxewa

BABI NA HUXU
4.0 Shimfixa
4.1 – Canje canje da ake samu a miyar gargajiya
4.2 – Canje canje da ake samu a miyar zamani
4.3 – Kammalawa
4.4 – Manazarta

BABI NA XAYA
1.0      GABATARWA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maxaukakin sarki wanda ya halicci mutum da aljan, ya kuma yi wa xan Adam baiwa wadda bai yi wa sauran halittunsa ba wato ya hore masa harshe domin sadarwa. Wannan aikin zai yi tsokaci ne a kan bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani. Don haka na sanya wa wannan aikin nawa suna “Bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.”

Bugu da qari, na yi qoqarin karkasa wannan aikin har zuwa babi huxu (4). A babi na farko na yi qoqarin gabatar da littafin, abin da Hausawa ke kira waiwaye adon tafiya, wato bitar ayyukkan da suka gabata. Na kalli wasu ayyukkan da Magabata suka yi a kan sana’o'in Hausawa domin ganin inda suka tsaya da kuma dacewa da ci gaba da wannan bincike. Bayan wannan kuma, na yi qoqarin nuna hanyoyin da wannan aikin nawa ya bi domin samun haske na ci gaba da bincike. Daga nan kuma sai muhallin bincike wato iyakokin da wannan bincike zai tsaya, sai kuma muhimmancin bincike duk domin ganin kwalliya ta biya kuxin sabulu.

A babi na biyu na yi qoqarin kawo ma’anar miya, da kuma kayayyakin da ake amfani da su wajen haxa miyar gargajiya da ta zamani. Na uku na yi qoqarin kawo bayani a kan yadda ake dafa miyar gargajiya da ta zamani, a nan ne na yi qoqarin nuna bambanci da kamance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.

A babi na huxu na kawo canje-canjen da ake samu tsakanin miyar gargajiya da ta zamani kuma a nan ne na kammala aikin nawa ta kawo irin bambanci da kammance tsakanin miyar gargajiya da ta zamani.

1.1      Bitar ayyukan da suka gabata.
Abu ne da ya wajaba ga kowane irin bincike irin wannan ya yi waiwaye dangane da nazarce-nazarcen da aka gabatar a fagen bincike don ganin abin da masana da manazarta suka gudanar a fagen bincike, wato ko dai a xora a kan wata a qara wa Borno dawaki, hujjar ita ce ban samu wani aiki makammancin nawa ba. A wannan bincike nawa ba’a tsallake irin wannan tsari ba, don haka, na samu karanta wasu aikace aikacen da suka gabata kamar haka;

Murtala Maikuxi da Umaru Haruna Mayana 1989- 1990 Miyar gargajiya ta da da Hausawa ke yi, kundin digirin su na farko....

For more Hausa Projects click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Attribute: 61 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Price: N3,000  |  Delivery: Within 2hrs
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Select Your Department

Featured Post

Reporting and discussing your findings

This page deals with the central part of the thesis, where you present the data that forms the basis of your investigation, shaped by the...

Followers